Featured
Masu Ciwon Hanta Sun Fi Yawa a Jihohin Katsina, Taraba Da Neja – Rahoto
Wani sabon rahoto na Ma’aikatar Lafiya ya bayyana cewa mutane 12,060 a Najeriya sun kamu da cututtukan Hepatitis B da C bayan da aka gwada mutane 210,947 a jihohi 12 na ƙasar. Rahoton ya nuna cewa yawancin waɗanda aka gano suna ɗauke da cutar ba su fara shan magani ba, duk da cewa Hepatitis na iya jawo matsanancin ciwon hanta da mutuwa idan ba a dauki mataki da wuri ba. WHO ta ce cututtukan Hepatitis na daga cikin manyan cututtukan da ke kashe mutane a duniya, inda suke hallaka fiye da miliyan ɗaya a kowace shekara.
Rahoton ya yi bayani dalla–dalla kan yadda aka gudanar da gwaje-gwajen a jihohin, inda Kano ta yi gwajin mutane mafi yawa – 28,461, kuma 2,231 daga cikinsu sun fito masu dauke da HBV. Nasarawa ma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, inda aka gano 3,348 masu dauke da cutar HBV daga cikin 38,035 da aka gwada. Wasu jihohi kamar Katsina, Taraba da Niger sune jihohin da aka fi samun wadanda suka kamu da cutar, inda aka samu kashi 18%–19% cikin waɗanda aka gwada suna dauke da cutar.
A cikin wannan bincike, Kakaki24 ta gano cewa jihohin da suka fi samun waɗanda suka kamu da Hepatitis ba lallai su ne suka fi yawan jama’a ba, amma rashin samun magani da ƙarancin wayar da kai na kara ta’azzara matsalar. Rahoton ya kara jaddada cewa cakuda rashin magani da ƙarancin dubawa na nufin cewa dubban masu fama da cutar na iya kasancewa a cikin al’ummar ƙasar ba tare da sanin halin da suke ciki ba.
Masana sun yi kira ga gwamnati da cibiyoyin lafiya da su kara yawan gwaji, rage tsadar magani, tare da wayar da kan jama’a kan cututtukan Hepatitis B da C. Ana ganin cewa fadada gwaje-gwaje da bayar da magani cikin lokaci za su taimaka wajen rage mace-mace da kare lafiyar jama’a a Najeriya.
