Connect with us

Featured

Engr. Farouk Ahmed Ya Yi Murabus Daga Muƙamin Shugaban Hukumar NMDPRA

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawan Najeriya sunayen sababbin shugabanni biyu da ya zaɓa domin jagorantar hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa (NMDPRA) da kuma hukumar kula da hako mai ta ƙasa (NUPRC), bayan murabus ɗin Injiniya Farouk Ahmed da Gbenga Komolafe. Wannan mataki ya zo ne a ranar Talata, 17 ga Disamba, 2025.

Farouk Ahmed da Gbenga Komolafe sun samu naɗin shugabancin hukumomin a shekarar 2021 a zamanin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, bayan kafa su ƙarƙashin Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA). Shugaba Tinubu ya bukaci majalisar ta gaggauta tantancewa da amincewa da sababbin sunayen da ya miƙa.

A cewar bayanin da Kakaki24 ta samu, Tinubu ya naɗa Oritsemeyiwa Amanorisewo Eyesan a matsayin Shugabar Hukumar NUPRC, yayin da Injiniya Saidu Aliyu Mohammed ya zama sabon Shugaban Hukumar NMDPRA. Dukansu an bayyana su a matsayin gogaggun kwararru da suka shafe shekaru masu yawa a harkar mai da iskar gas.

Eyesan ta kammala karatun Tattalin Arziki a Jami’ar Benin, inda ta yi kusan shekaru 33 a NNPC, har ta yi ritaya a matsayin Mataimakiyar Shugaba (Upstream). A ɓangaren Saidu Mohammed kuwa, wanda ya kammala karatun Injiniyan Kimiyya a Jami’ar Ahmadu Bello, ya taɓa rike muƙamai masu muhimmanci a NNPC, ciki har da jagorantar manyan ayyukan gas kamar AKK Pipeline da Escravos–Lagos Pipeline Expansion.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet