Featured
Burkina Faso Ta Sako Sojojin Najeriya 11 Da Ta Tsare
Gwamnatin ƙasar Burkina Faso ta sako sojojin Najeriya 11 tare da jirgin sojan saman Najeriya (NAF C-130), kwanaki goma bayan da aka tsare su sakamakon saukar gaggawa da jirgin ya yi a birnin Bobo-Dioulasso. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya tabbatar da sakin a daren Laraba, inda ya ce an tabbatar masa da hakan daga ofishin jakadancin Najeriya da ke Burkina Faso.
An tsare sojojin da jirgin ne a ranar 8 ga Disamba, 2025, bayan jirgin ya samu matsalar fasaha jim kaɗan bayan tashinsa daga Lagos yana kan hanyarsa zuwa Portugal, lamarin da ya tilasta masa sauka a ƙasar Burkina Faso. Hukumomin ƙasar sun zargi jirgin da karya dokar sararin samaniyarsu, suna cewa bai samu izinin shiga ba, abin da suka bayyana a matsayin tauye ikon ƙasarsu.
Bayan tsawon tattaunawar diflomasiyya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike da Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, a matsayin wakili na musamman zuwa Ouagadougou, domin sasanta lamarin. Rundunar Sojin Saman Najeriya ta sha tabbatar da cewa sojojin na cikin koshin lafiya kuma an yi musu mu’amala mai kyau yayin tsarewar, yayin da Majalisar Wakilai ta ƙasa ta nuna damuwa tare da kira da a gaggauta sakin su. Har yanzu dai ba a bayyana ranar da za a dawo da sojojin da jirgin zuwa Najeriya ba.
