Featured
Burkina Faso ta dawo da hukuncin kisa bayan shafe shekaru takwas da soke shi
Gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ƙarƙashin jagorancin Kaftin Ibrahim Traoré, ta dawo da hukuncin kisa, wanda aka soke tun shekarar 2018.
Sabuwar dokar ta tanadi hukuncin kisa ga waɗanda aka samu da laifukan ta’addanci, leƙen asiri, cin amanar ƙasa da kuma kashe iyaye.
Haka kuma, dokar ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya shigo da kayayyakin da wa’adin amfaninsu ya ƙare ko kuma haramtattun kayayyaki, idan sun haddasa mutuwar wani mutum.
Wannan mataki na nufin Burkina Faso ta sake amincewa da amfani da hukuncin kisa a matsayin hukuncin wasu manyan laifuka, bayan shafe shekaru takwas tun bayan soke shi.
