Connect with us

Featured

Burkina Faso Ta Kama Jirgin Sojin Najeriya Bayan Ya Keta Sararin Samaniyar Ƙasar

A ranar Litinin, gwamnatin Burkina Faso ta bayyana cewa ta tilasta wa wani jirgin saman sojin Najeriya sauka a ƙasarta bayan an gano ya keta sararin samaniyarta ba tare da izini ba. Jirgin, wanda ya ƙunshi ma’aikata biyu da fasinjoji tara, jirgin ya shiga ƙasar ne a cewar hukumomin tsaron Burkina Faso ba tare da wata sanarwa ko izinin shawagi ba.

Sanarwar gwamnati ta nuna cewa binciken farko ya tabbatar da cewa jirgin ba ya da sahihin izinin wucewa, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka umarci matuƙansa da su sauka nan take. Hukumar ta kuma bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da ƙarin bincike kan dalilin da ya sa jirgin ya shiga yankin ba bisa ka’ida ba.

Ƙungiyar AES ta yi Allah-wadai da abin da ta kira keta haddin ƙasashe, tana mai jaddada cewa za ta ɗauki mataki kan duk wani jirgi da ya kutsa cikin sararin samaniyar kowace ɗaya daga cikin ƙasashen yankin ba tare da izini ba. Ƙungiyar ta ce irin waɗannan lamurra barazana ne ga tsaro da mutuncin ƙasashen yankin.

Har yanzu dai babu wata sanarwa daga rundunar sojin saman Najeriya ko gwamnatin tarayya game da wannan lamari. Ana sa ran hukumomin Najeriya za su yi bayani kan abin da ya faru yayin da tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu ke ci gaba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet