Connect with us

Featured

JAMB Za Ta Tantance Cibiyoyin CBT 1,039 Domin Jarrabawar UTME Ta 2026

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta ƙasa (JAMB) ta bayyana shirin tantance cibiyoyin jarabawar kwamfuta (CBT) guda 1,039 a faɗin Najeriya domin UTME na shekarar 2026. Shugaban hukumar, Farfesa Is’haq Oloyede, ya bayyana hakan a ranar Laraba, 18 ga Disamba 2025, yayin da yake jagorantar rangadin tantance cibiyoyin CBT a Ilorin, Jihar Kwara.

Oloyede ya ce an tura ƙungiyoyin tantancewa 52 zuwa jihohi daban-daban domin sabunta tantance cibiyoyin da suka cika ƙa’ida ko kuma cire waɗanda suka gaza. Ya jaddada cewa amincewar da aka bayar a shekarar da ta gabata ba ta nufin cibiyar za ta ci gaba da cancanta ba, yana mai cewa JAMB ta ƙara tsaurara matakai kan cibiyoyin da aka samu da laifin tafka maguɗi a baya.

Ya ƙara da cewa hukumar ta haɗa kai da Hukumar CAC, inda ta kulle bayanan masu cibiyoyin da aka haramta, tare da toshe NIN na masu laifi da ma’aikatan da suka yi hannu a maguɗi. Haka kuma, duk kwamfutocin da aka yi amfani da su a cibiyoyin da aka cire ba za su ƙara shiga tsarin JAMB ba, yayin da jami’an tsaro ke bincike kan duk wata karya doka, domin tabbatar da sahihanci da adalci a jarabawar UTME mai zuwa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet