Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Kashe Naira Biliyan 32.9 Don Inganta Cibiyoyin Kula da Lafiya a Matakin Farko
Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da Naira biliyan 32.9 na zangon ƙarshe na shekarar 2025 ta hannun Asusun Tallafa Lafiyar Asali (BHCPF), domin ƙarfafa ayyukan kula da lafiya a matakin farko da kuma faɗaɗa inshorar lafiya a jihohi 36 na ƙasar.
Sakatariyar dindindin a Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, Daju Kachollom, ta ce za a fara rabon kuɗaɗen a Janairu 2026, inda ta bayyana cewa hakan na nuna ƙudurin gwamnati na inganta tsari, gaskiya da walwala a harkar lafiya.
Hukumar Kula da Lafiyar Asali ta Ƙasa ta ce sabon tsarin zai bai wa cibiyoyi kuɗi bisa yawan marasa lafiya, inda ƙananan cibiyoyi za su rika karɓar N600,000, manya kuma N800,000 a kowane zangon wata uku, domin ƙara ingancin hidima da rage kuɗin da jama’a ke kashewa daga aljihunsu.
