Featured
Ba-gudu-ba-ja-da-baya : Sabbin Dokokin Haraji Za Su Fara Aiki 1 ga Janairu — Oyedele
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa sabbin dokokin haraji biyu da aka rattaba hannu a kansu za su fara aiki daga 1 ga Janairu 2026, duk da cece-kucen da ake yi kan zargin sauya wasu sashe, in ji Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Sauya Tsarin Haraji, Taiwo Oyedele.
Oyedele ya ce dokokin harajin na da tasiri kai tsaye ga talakawa, inda kashi 98 cikin 100 na masu ƙaramin albashi za su rika biyan haraji ƙasa ko kuma ba za su biya PAYE ba kwata-kwata, yayin da ƙananan ’yan kasuwa da dama za su samu rangwamen haraji.
A halin da ake ciki, Majalisar Tarayya ta fara binciken cikin gida kan yadda aka wallafa dokokin a mujallar gwamnati, tare da bayar da umarnin sake fitar da su da kuma bai wa jama’a Certified True Copies (CTC), tana mai cewa matakin na gudanarwa ne kawai don tabbatar da sahihancin abin da majalisa ta amince da shi.
