Featured
Shettima Ya Tabbatar Wa Ƴan Najeriya Cewa Gwamnatin Tarayya Za Ta Kawo Ƙarshen Ta’addanci a Faɗin Ƙasar
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ƙasar nan za ta yi galaba kan ta’addanci tare da dawo da zaman lafiya, yayin ziyararsa ga waɗanda suka tsira daga harin bam a masallacin Gamboru Market da ke Maiduguri, Jihar Borno, a ranar Juma’a.
Shettima ya kai ziyarar ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inda ya miƙa ta’aziyyar Shugaba Bola Tinubu, yana mai jaddada aniyar gwamnatin tarayya na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da cewa hare-haren ta’addanci za su zo ƙarshe da yardar Allah.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya kashe mutum biyar, yayin da wasu ke karɓar magani, lamarin da Mataimakin Shugaban Ƙasar ya yabawa Gwamna Babagana Zulum bisa ƙoƙarinsa, yana mai cewa gwamnatin tarayya da ta jihar Borno na aiki tare domin shawo kan matsalolin tsaro a yankin Arewa maso Gabas.
