Connect with us

Featured

Ana Fargabar Amurka Ta Kai Wani Hari Kwara

Fargaba ta mamaye al’ummar garin Offa da ke jihar Kwara a daren Alhamis, 25 ga Disamba, 2025, bayan wasu abin fashewa sun girgiza sassan garin, lamarin da ya lalata kadarori tare da tayar da hankalin jama’a. Lamarin ya faru ne a wurare biyu daban-daban, inda aka ce fashewar ta farko ta afku a yankin filin sallar Idi, yayin da ta biyu ta faru kusa da otal ɗin Solid Worth

Rahotanni sun nuna cewa an gano wani abu mai fashewa da bai tashi ba a wurin na biyu, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka killace yankunan domin gudanar da bincike. Shugaban karamar hukumar Offa, Suleiman Olatunji Omituntun, ya ziyarci wuraren da abin ya shafa, yayin da kakakin karamar hukumar ya bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da dogaro da sahihan bayanai kadai yayin da bincike ke gudana.

Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa PUNCH cewa abin da ya fado a Offa wani bangare ne na makamin roka (missile) da aka harba a hare-haren sama na Amurka a arewa maso yammacin Najeriya, musamman a jihar Sokoto, inda aka kai farmaki kan ‘yan ta’adda. Duk da haka, har yanzu babu cikakken bayani a hukumance da ke danganta fashewar Offa kai tsaye da hare-haren, yayin da ‘yan sanda suka tabbatar da cewa bincike na musamman na ci gaba, kuma ba a samu rahoton rasa rai ba zuwa yanzu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet