Connect with us

Featured

Ƴanbindigar Da Suka Yi Garkuwa Da Masu Ibada a Kwara Sun Nemi Miliyan 100 Kan Kowanne Mutum Ɗaya

A kalla mutum 30 zuwa 35 ne aka yi garkuwa da su yayin harin da ’yan bindiga suka kai cocin Christ Apostolic Church (CAC) da ke Eruku a jihar Kwara da daren Talata, inda suka nemi N100m a kan kowanne mutum. Faston cocin, Lawrence Bamidele, ya tabbatar da cewa maharan sun shigo cikin cocin lokacin ibada suka yi awon gaba da masu bautar Allah ba tare da tsoro ba.

A cewar majiyoyi, masu garkuwar sun fara kiran iyalan waɗanda aka sace ta wayoyinsu, domin neman kuɗin fansa. Sakataren cocin, Josiah Agbabiaka, ya ce an shaida musu cewa rukunin farko mai mutum 11, an buƙaci N100m ga kowanne. Basaraken yankin, Olori Eta, Cif Olusegun Olukotun — wanda ’yan uwansa huɗu na cikin waɗanda aka tafi da su — ya ce shi ya tsere ta taga yayin harin.

A yayin tabbatar da lamarin, Kakaki24 ta tattaro cewa ’yan bindigar suna ci gaba da kiran iyalan waɗanda aka sace ɗaya bayan ɗaya, duk da cewa rundunar ’yan sanda ta jihar ta ce har yanzu babu wani rahoto na hukumance da ya nuna ana neman kuɗin fansa. Rundunar ta bayyana cewa jami’anta tare da sojoji na ci gaba da aikin ceto ba tare da gajiyawa ba.

Rundunar ’yan sanda ta Kwara, ta bakin kakakinta SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta roƙi al’umma da su ci gaba da tura bayanai masu amfani da za su taimaka wajen kubutar da waɗanda aka sace cikin gaggawa. Hakan na zuwa ne yayin da jama’a ke ci gaba da fargabar tsaron yankin da kuma halin da waɗanda aka yi garkuwa da su ke ciki.

Fri, 21 Nov 2025 – 7:05am

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet