Featured
NSCDC Ta Kama Mutane 8 Da Ake Zargi Da Hannu Wajen Kai Wa Ofishinta Hari
Rundunar Tsaro ta NSCDC a Jihar Katsina ta bayyana cewa ta kama mutane takwas da ake zargi da hannu a harin da aka kai wa wani ofishinta a Koraman Nayalli, cikin birnin Katsina. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SC Buhari Hamisu, ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na NAN a ranar Litinin.
Hamisu ya ce harin ya faru ne a ranar Lahadi, bayan wasu matasa sun yi zanga-zanga sakamakon wani samame da ya kai ga mutuwar wani da ake zargin dillalin miyagun ƙwayoyi mai suna Uzairu, wanda aka fi sani da Dan’kuda. Ya ce masu tarzomar sun banka wa ginin ofishin wuta tare da ƙona babura uku da wasu kayayyaki.
Ya ƙara da cewa masu tarzomar, dauke da makamai masu haɗari, sun kuma kai ziyara wasu ofisoshin NSCDC da ‘yan sanda a Filin Kanada kafin jami’an tsaro su shawo kan lamarin. Kwamandan NSCDC na jihar, Abbas Moriki, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi tare da kafa kwamitin mutum bakwai domin gano gaskiyar abin da ya faru.
