Featured
Wani Abin Fashewa Ya Tashi a Babban Asibitin Kebbi
An jiyo ƙarar tashin wani abin fashewa mai ƙarfi , wanda ya tayar da hankula a yankin Bagudo na Jihar Kebbi da safiyar Talata, 30 ga Disamba, 2025, a Babban Asibitin jihar. Lamarin ya jefa jama’a cikin fargaba a yankin da ke kusa da asibitin.
Bayan faruwar lamarin, an tura haɗin gwiwar jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda, sojoji da ‘yan sa-kai zuwa wurin. Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ƙungiyar ƙwararru ta EOD-CBRN na gudanar da cikakken bincike a asibitin domin tantance halin da ake ciki.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Kebbi, SP Bashir Usman Anisma, ya tabbatar da cewa babu asarar rai, sai dai wani gini a barikin ma’aikatan asibitin ya lalace. Ya ƙara da cewa an ƙara yawan jami’an tsaro a yankin, tare da roƙon jama’a da su kwantar da hankalinsu su kuma guji kusantar wurin yayin da bincike ke gudana.
