Featured
Wutar Lantarki Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 38 – NERC
Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta bayyana cewa mutane 38 sun mutu sakamakon haɗurran da suka shafi wutar lantarki a zango na uku na shekarar 2025. Rahoton ya nuna cewa adadin ya ƙaru idan aka kwatanta da mutane 33 da suka mutu a zangon da ya gabata.
A cewar NERC, dukkan mutuwar sun faru ne a matakin rarraba wutar lantarki, wanda aka bayyana a matsayin mafi haɗari ga al’umma. Duk da cewa adadin haɗurran ya ragu daga 60 zuwa 57, yawan waɗanda suka jikkata ya ƙaru daga 19 zuwa 33 a wannan lokaci.
Rahoton ya nuna cewa kamfanonin rarraba wuta (DisCos) ne kaɗai suka samu waɗannan haɗurra, inda Ikeja da Kano suka fi yawan asarar rayuka, sai Eko da Kaduna. NERC ta ce za ta ci gaba da sanya ido kan tsaro a bangaren wutar lantarki tare da ɗaukar matakan hukunci ga duk wanda ya karya ƙa’idojin lafiya da tsaro.
