Featured
APC Ta Yi Watsi Da Yunƙurin Tsige Gwamna Fubara
Jam’iyyar APC reshen jihar Rivers ta yi fatali da yunkurin da majalisar dokokin jihar ke shirin yi na tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu. Jam’iyyar ta ce duk da girmama ikon majalisa, ba za ta amince da matakin tsige gwamnan ba.
A wata sanarwa da ta fitar, APC ta bayyana shirin tsige gwamnan a matsayin yunƙurin “tayar da hargitsi” a jihar. Ta kuma yi kira ga ’yan majalisar dokokin jihar da su kauce wa duk wani mataki da zai jefa Rivers cikin sabon rikicin siyasa.
Majalisar dokokin jihar ta ƙaddamar da yunkurin tsige gwamnan ne a ranar Alhamis bisa zargin aikata laifukan da suka saɓa ƙa’idar aiki. Lamarin na zuwa ne bayan Gwamna Fubara ya koma APC a watan da ya gabata, a ci gaba da rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar tun bayan zaɓen 2023.
