Featured
Kotu Ta Yi Watsi Da Tuhumar Da Gwamnatin Tarayya Ta Shigar Kan Sanata Natasha
Babbar Kotun Birnin Tarayya (FCT) da ke Abuja ta yi watsi da tuhumar laifi da Gwamnatin Tarayya ta shigar kan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya. Matakin dai ya biyo bayan janye karar da Ofishin Babban Lauyan Ƙasa (AGF) ya yi a gaban kotun.
Takardun kotu sun nuna cewa AGF ya shigar da Notice of Discontinuance, wanda ya kawo ƙarshen tuhume-tuhumen ɓata suna da sauran laifuka da aka jingina wa sanatar.. Shari’ar, wadda ta samo asali daga wasu kalamai da ake zargin ta yi a yayin wata hira da wani gidan talabijin, ta jawo muhawara a ƙasa kan ‘yancin faɗar albarkacin baki da alhakin ‘yan siyasa.
Alkalin shari’ar, Mai shari’a C. N. Oji, ya amince da janyewa karar tare da yanke hukuncin watsar da ita. Bayan shari’ar, Sanata Natasha ta bayyana hukuncin a matsayin nasara da tabbatar da gaskiyarta, tana mai cewa za ta ci gaba da mai da hankali kan ayyukan majalisa da hidima ga al’ummar Kogi ta Tsakiya.
