Addini
Sarkin Musulmi Ya Bayar da Umarnin Duban Jinjirin Watan Sha’aban 1447 AH
Majalisar Masarautar Sakkwato ta umarci al’ummar Musulmi a fadin Najeriya da su fara duban jinjirin watan Sha’aban 1447 AH a ranar Litinin, 19 ga Janairu, 2026. An bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar wadda Wazirin Sakkwato kuma Shugaban Kwamitin Shawara kan Harkokin Addini, Farfesa Sambo Junaidu, ya sanya wa hannu, ta ce ranar Litinin ta yi daidai da 29 ga watan Rajab 1447 AH, wanda shi ne lokacin duban jinjirin wata bisa koyarwar Musulunci.
Majalisar ta bukaci Musulmi su taka rawar gani wajen duban jinjirin tare da kai rahoton duk wani sahihin gani ga hakiman gunduma ko na kauye domin isarwa ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, tare da yin addu’ar Allah Ya ba da nasara a wannan ibada.
