Addini
Sarkin Musulmi Ya Ayyana Talata a Matsayin 1 Ga Watan Sha’aban 1447AH
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, CFR, mni, kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya ayyana Talata, 20 ga Janairu, 2026 a matsayin ranar farko ta watan Sha’aban 1447 bayan Hijira.
Sanarwar ta fito ne cikin wata takarda ta musamman da aka fitar a ranar Litinin, 19 ga Janairu, 2026, bayan samun rahotannin ganin jinjirin watan Sha’aban a wasu sassan ƙasar.
Takardar sanarwar ta samu sa hannun Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sakkwato kuma Shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Addini na Fadar Sarkin Musulmi, inda ya bukaci al’ummar Musulmi su yi amfani da watan wajen ƙara ibada da kyawawan ayyuka.
