Featured
Gwamna Yusuf Ya Gana da Tinubu Kan Tsaro da Manyan Ayyuka – Sanusi Bature
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi wata ganawar sirri da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar 20 ga Janairu, 2026, inda ya gabatar da muhimman buƙatun gwamnatinsa da suka shafi tsaro, manyan ayyukan more rayuwa da haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya.
A cewar sanarwar da Mai Magana da Yawun Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu, gwamnan ya yi wa Shugaban Ƙasa bayani kan ƙalubalen tsaro da ke ƙara kamari a wasu ƙananan hukumomin Kano. Yana mai jaddada buƙatar ƙarin tallafin tarayya domin kare rayukan al’umma.
Gwamna Yusuf ya kuma tattauna batun manyan ayyukan ci gaba, inda ya gode wa Shugaban Ƙasa kan sa hannu akan aikin titin Wujuwuju, yana mai bayyana shi a matsayin muhimmin mataki ga bunƙasar tattalin arziƙi. Shugaba Tinubu ya tabbatar da aniyar Gwamnatin Tarayya ta haɗa hannu da Kano wajen yaƙi da rashin tsaro da kuma bunƙasa ci gaba mai ɗorewa.
