Featured
Kotu Ta Wanke Mahadi Shehu Daga Dukkan Tuhume-tuhumen Da Ake Masa
Kotun Tarayya dake zamanta a Kano ta wanke kuma ta sallami ɗan gwagwarmaya kuma mai sharhi kan al’amuran jama’a, Muhammad Mahadi Shehu, tare da kamfaninsa Dialogue Global Links Limited, daga dukkan tuhume-tuhume guda shida da Ofishin babban Sufeta Janar na ’Yan Sanda ya shigar a kansu a madadin tsohuwar Gwamnatin Jihar Katsina.
An shigar da tuhume-tuhumen ne tun a shekarar 2021, inda suka shafi zargin aikata laifukan bata suna ta kafofin zamani da yaɗa takardun bogi, da kuma watsa bayanan ƙarya da ake zargin sun jawo damuwa ga jami’an Gwamnatin Jihar Katsina.
Da yake karanta hukunci mai shafuka 70 wanda ya ɗauki kusan sa’o’i biyu, alkalin da ya jagoranci shari’ar, Mai shari’a Simon Amobeda, ya ce masu gabatar da ƙara sun gaza kafa hujjar farko akan waɗanda ake ƙara.
Kotun ta bayyana shaidun masu gabatar da ƙarar a matsayin marasa tabbas, inda ta yanke cewa ba a tabbatar da ko ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen guda shida babu shakku ba.
Masu gabatar da ƙarar sun kira shaidu guda shida daga Ofishin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da Gwamnatin Jihar Katsina akan ƙarar.
Shugaban tawagar lauyoyin Mahadi Shehu, Barrista Mustapha Abubakar, SAN ya yabawa Mai shari’a Amobeda kan abin da ya kira hukunci dauke da zurfin tunani, wanda ya tabbatar da bin doka da ’yancin bangaren shari’a.
Da yake zantawa da ’yan jarida jim kaɗan bayan hukuncin, Mahadi Shehu ya ce shari’ar ta ɗauki kusan shekaru huɗu, ta hannun alkalai huɗu, kuma yana nan akan gwagwarmayarsa.
Haka kuma, ɗaya daga cikin lauyoyin masu gabatar da ƙarar, Barrista Badamasi Garba, ya ce za su yi nazari akan tabbacen kwafin hukuncin da kotu ta tabbatar kafin su yanke shawara kan mataki na gaba.
Wannan hukunci ya kawo ƙarshen shari’ar da ake yi wa Mahadi Shehu da kamfaninsa da ta ja hankalin ƙasa baki ɗaya tun daga shekarar 2021.
