Featured
Ba a Iya Faɗawa Masu Mulki Gaskiya a Gwamnatin Tinubu – Gwamnan Oyo
Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce abu ne mai wahala a faɗi gaskiya ga masu mulki a ƙarƙashin gwamnatin tarayya ta yanzu, inda ya kwatanta hakan da lokacin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da ya ce ana samun tattaunawa da shawarar juna. Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a birnin Ibadan.
Gwamnan ya yi jawabin ne yayin bikin cikar Fasto Samson Ajetomobi shekara 60 da haihuwa, inda ya tuna rawar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya taka a lokacin annobar COVID-19. Ya ce shugabancin Osinbajo a Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa (NEC) ne ya sa Oyo ba ta shiga cin jihohin da aka kulle a 2020 ba.
Makinde ya soki yadda gwamnatin yanzu ke tafiyar da batun kudirin gyaran haraji, yana zargin ta da rufe ƙofofi ga ra’ayoyin masu suka. Ya ce sun nemi a dawo da kudirin domin tattaunawa, amma aka ƙi sauraro, yana mai jaddada cewa “ba za ka iya faɗin gaskiya ga masu mulki a wannan zamani ba.”
