Connect with us

Featured

Sojoji Sun Gano Masana’antar Ƙera Makamai a Nasarawa

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta na Operation WHIRL STROKE (OPWS) sun gano wata masana’antar ƙera makamai ba bisa ƙa’ida ba da ke ɓoye a yankin Agwatashi, ƙaramar hukumar Doma a Jihar Nasarawa. An gano wurin ne yayin sintiri da sojoji ke yi domin hana masu aikata laifuka samun ‘yancin motsi.

Sanarwar da rundunar ta fitar a shafinta na X ta ce wurin na samar da makamai ga masu aikata laifuka a yankin da ma wajensa. Da isar sojoji, wasu da ake zargi sun tsere, amma an kama mutum ɗaya ɗan shekara 26 daga ƙauyen Arusu a ƙaramar hukumar Kokona yayin da yake ƙoƙarin tserewa ta hanyar ɓoyewa a kan wata bishiya.

Bincike ya kai ga gano bindigogi guda shida da aka ƙera tare da kayan aiki da na’urorin ƙera makamai, kuɗi da wayar salula. Kwamandan rundunar, Manjo Janar Moses Gara, ya bukaci sojoji su ci gaba da dogaro da sahihan bayanan sirri, tare da kira ga al’umma da su ba jami’an tsaro haɗin kai domin tabbatar da tsaro mai ɗorewa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet