Featured
Kotu Ta Dakatar da Yajin Aikin Ma’aikatan Abuja
Kotun warware matsalolin ƴan ƙwadago ƙarƙashin jagorancin Alƙali Emmanuel Subilim ta umarci ma’aikatan babban birnin tarayya FCTA da su dakatar da yajin aikin da suke yi. Kotun ta ce dole ne a dakatar da yajin aikin har sai ta saurari ƙarar da aka shigar a gabanta.
Wannan umarni ya biyo bayan buƙatar Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, wanda ya nemi kotun ta tilasta wa ma’aikatan da ke yajin aikin su koma bakin aiki. A cikin ƙarar, Wike ya sanya shugaba da sakataren haɗakar ƙungiyar ƴan ƙwadago JUAC a matsayin waɗanda ake ƙara.
Alƙalin ya bayyana cewa duk lokacin da aka shigar da ƙara a gaban kotun warware matsalolin ƴan ƙwadago, wajibi ne a dakatar da yajin aiki domin ba da damar warware matsalar. Ya kuma gargadi cewa rashin bin wannan doka na iya jawo hukunci, yayin da kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 25 ga Maris, 2026.
