Featured
Babu Ƙasar da Kullum Ake Kashe Al’ummarta Kamar Najeriya – Kukah
Bishop na Cocin Katolika na Sokoto, Matthew Kukah, ya bayyana damuwa kan yawaitar kashe-kashe a Najeriya, yana cewa babu wata ƙasa a duniya da ke fuskantar irin haka a kullum. Kakah Ya faɗi hakan ne a Yola, Jihar Adamawa, yayin ƙaddamar da littafi kan Gwamna Ahmadu Fintiri.
Matthew ya ce ƙasar na fuskantar rabuwar kai saboda addini, lamarin da ke ƙara tsananta rikici, inda ya zargi kafofin watsa labarai na ƙasashen waje da ƙara hura wutar bambancin addini. A cewarsa, a Najeriya ne kaɗai ake kiran mutuwa da sunan Kirista ko Musulmi, lamarin da ke hana ƙasar ci gaba.
Ya yi kira ga shugabannin siyasa da na addini da su gina tsare-tsare da cibiyoyi da za su haɗa kan ‘yan ƙasa domin samar da zaman lafiya da cigaba.
