Featured
Tawagar Sojojin Amurka Ta Sauka a Najeriya – Ministan Tsaro
Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatar wa BBC cewa wata ƙaramar tawagar sojojin Amurka tana aiki a Najeriya, inda za su bayar da horo ga sojojin ƙasar domin inganta ayyukan tsaro.
Ministan bai bayyana yawan sojojin, lokacin isarsu, inda za a jibge su, ko tsawon lokacin da za su zauna ba. Sai dai ya bayyana cewa aikin sojojin zai ta’allaka ne kan bayar da tallafi a fannin tattara bayanan sirri.
Shugaban sojin Amurka a Afirka, AFRICOM, Janar Dagvin R. M. Anderson, ya ce tura sojojin Amurka zuwa Najeriya ya faru ne bisa buƙatar gwamnatin Najeriya, domin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen tattara bayanan sirri da yaƙi da ta’addanci.
Najeriya ta ƙara haɗin gwiwa da Amurka a wannan lokaci, yayin da take fama da hare-haren ‘yan bindiga, sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa, da kuma yaɗuwar kungiyoyin ta’addanci a wasu yankuna.
