Featured
’Yan Sanda Sun Kama Matashi Da Laifin Yin Damfara Ta Naira Miliyan 48.5 a Filin Jirgin Saman Lagos
Rundunar ’yan sandan filin jirgin sama a Lagos ta kama wani matashi mai shekara 24, Precious Onudhona, bisa zargin damfara ta N48.5m, kwatankwacin dala $35,000. Rundunar ta ce kamen na daga cikin ƙoƙarinta na hana aikata laifuka a filayen jiragen sama.
Kakakin rundunar, ASP Adeola Mohammed, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 2 ga Fabrairu 2026 a filin jirgin Murtala Muhammed, yayin da yake shirin tafiya Asaba a Jihar Delta. Bincike na farko ya nuna cewa ya shiga harkar damfara tun 2023 bayan shiga wata ƙungiya da ke yaudarar mutane ta soyayya a kafafen sada zumunta.
Rahoton ya ce wanda ake zargin yana amfani da sunan ƙarya “Travis Kevin,” inda ya ƙirƙiri shafin banki na bogi domin yaudarar mutane. Rundunar ta ce za a miƙa shi sashen Interpol domin ci gaba da bincike da gurfanarwa, tare da neman sauran mambobin ƙungiyar.
