Featured
CBN Ta Ƙayyade Shekaru 18 Domin Yin Rajistar BVN
Babban Bankin Najeriya, Central Bank of Nigeria (CBN), ya fitar da sabbin dokoki ga bankuna da cibiyoyin kuɗi domin ƙarfafa tsaron biyan kuɗi ta yanar gizo da kuma inganta tsarin lambar tantance asusun banki ta Bank Verification Number (BVN). Daga cikin sababbin dokokin, bankin ya kayyade cewa dole mutum ya kai shekaru 18 kafin a yi masa rajistar BVN.
CBN ya kuma ba abokan hulɗar bankuna damar dakatar da tura kuɗi ta gaggawa daga asusunsu idan sun ga dama. Haka kuma ya umarci bankuna su sanya karin matakan tsaro, ciki har da tantance mai asusu da hanyoyi kamar na’urar tabbatarwa da bayanan halittu, domin rage damfarar kuɗi ta yanar gizo.
Sabbin dokokin sun kuma tanadi cewa idan aka bude manhajar banki a sabuwar waya, iyakar kuɗin da za a iya tura wa cikin awanni 24 na farko ba za su wuce naira 20,000 ba. CBN ya ce waɗannan matakai za su fara aiki daga ranar 1 ga Yuli, 2026, yayin da sabuwar dokar BVN za ta fara aiki daga ranar 1 ga Mayu, 2026.
