Featured
NBC Ba Ta Da Hurumin Cin Tarar Gidajen Radiyo da Talabijin – Kotu
Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da National Broadcasting Commission (NBC) ta shigar, inda take neman a rusa hukuncin babbar kotun tarayya da ya hana ta cin tarar gidajen rediyo da talabijin a ƙasar.
A hukuncin da Mai Shari’a Oyebiola Oyewumi ta jagoranta a madadin alkalan kotun uku, an tabbatar da sahihancin hukuncin baya, wanda ya hana NBC cin tarar gidajen labarai 45 tun ranar 1 ga Maris 2019 bisa zargin karya dokokin yaɗa labarai.
Kotun ta bayyana cewa NBC ba ta da hurumin cin tara, tana mai cewa a ƙarƙashin dokar Najeriya, kotu ce kaɗai ke da ikon hukunta wanda aka samu da laifi, ba wata hukuma ba. Tun da farko ma babbar kotun tarayya ta ayyana matakin NBC a matsayin wanda ya saɓa wa doka.
