Connect with us

Featured

Kotu Ta Samu Tsohon Ministan Lantarki Da Laifin Almundahanar Biliyan 33

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta samu tsohon ministan lantarki, Saleh Mamman, da laifuka 12 da suka shafi halasta kuɗaɗen haram da suka kai kimanin Naira biliyan 33. Mai shari’a James Omotosho ne ya bayyana hakan a zaman kotu na ranar Alhamis.

Kotun ta ɗage yanke hukunci zuwa ranar 13 ga watan Mayun 2026 saboda Saleh Mamman bai halarci zaman kotun ba lokacin da aka same shi da laifi. Hakan ya sa lauyan hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo SAN, ya roƙi kotun ta bayar da sammacin kamo shi domin tabbatar da cewa bai fice daga ƙasar ba kafin ranar yanke hukunci.

Saleh Mamman ya kasance ministan lantarki daga shekarar 2019 zuwa 2021 a gwamnatin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. A ranar 28 ga Afrilu na wannan shekarar ne kuma ya sayi fom ɗin neman takarar gwamnan jihar Taraba a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet