Featured
Zan Ɗauki Matakin Shari’a Kan Duk Wanda Ya Kuma Cewa Ina Goyon Bayan Ƴan Ta’adda – Sheikh Gumi
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Ahmad Gumi, ya ce wasu mutane masu ra’ayin kabilanci na amfani da hirarrakin da ya yi da kafafen yada labarai kan matsalar tsaro da ‘yan bindiga a Najeriya wajen yada bayanan da ba daidai ba a kansa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai ranar Asabar 23 ga watan Mayu, Sheikh Gumi ya bayyana cewa ana karkatar da maganganunsa ta hanyar son zuciya domin bata masa suna, duk da cewa manufarsa ita ce bayar da shawara kan hanyoyin shawo kan matsalar tsaro a kasar.
Malamin ya jaddada cewa bai taba goyon bayan ayyukan ‘yan bindiga a ko’ina cikin Najeriya ba, yana mai cewa daga yanzu zai dauki matakin shari’a a kan duk wanda ya sake alakanta shi da bayar da goyon baya ga ‘yan bindiga. Ya wallafa sanarwar ne a shafinsa na Facebook.
