Featured
Ƴan Najeriya Sun Kashe Naira Tiriliyan 9 Wajen Sayen Katin Waya Da Data a 2025 – Rahoto
Wani rahoto ya bayyana cewa kwastomomin manyan kamfanonin sadarwa guda hudu a Najeriya sun kashe kusan naira tiriliyan 9 wajen sayen kati da data a shekarar 2025. Rahoton ya nuna cewa MTN Nigeria ta samu sama da naira tiriliyan 5.3 daga kwastomominta miliyan 90.3, yayin da Airtel Nigeria ta samu kusan naira tiriliyan 3.1 daga masu amfani da layinta miliyan 60.9.
Rahoton ya ce karuwar kudaden shiga ta samo asali ne daga karin farashin kudin kira da data da Hukumar NCC ta amince da shi, tare da yawaitar amfani da intanet da wayoyin zamani. Haka kuma, an bayyana cewa yawan amfani da data a Najeriya ya karu matuka, inda ‘yan kasar ke amfani da kusan terabytes 45,800 na data a kullum.
Sai dai duk da karin kudaden da kamfanonin sadarwar suka samu, masu amfani da layukan waya sun koka kan rashin ingancin sabis. Shugaban kungiyar masu amfani da sadarwa ta kasa ya bukaci kamfanonin su yi amfani da ribar da suke samu wajen inganta hanyoyin sadarwa domin rage matsalolin da kwastomomi ke fuskanta.
