Featured
Jam’iyyar NDC Ta Tsayar da Aminu Abdussalam a Matsayin Ɗan Takarar Gwamna a Kano
Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran ƙungiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar da zaɓar Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a zaɓen shekarar 2027. Haka kuma ya bayyana cewa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna zai nemi kujerar sanatan Kano ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar.
Kwankwaso ya ce an ɗauki matakin ne bisa gaskiya, biyayya da ƙwarewa, waɗanda ya bayyana a matsayin ginshiƙan haɗin kan Kwankwasiyya da ci gaban jam’iyyar. Sanarwar ta fito ne bayan shafe kwanaki ana tattaunawa tsakanin jagororin Kwankwasiyya da manyan ‘yan siyasa a Kano kan shirye-shiryen zaɓen 2027.
Kwamared Aminu Abdussalam ya sauka daga muƙaminsa na mataimakin gwamnan Kano a watan Maris bayan rikicin siyasa da ya biyo bayan sauya sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC. Rahotanni sun nuna cewa rashin jituwar siyasa tsakanin bangarorin biyu ne ya haddasa saukar tasa daga muƙami.
