Featured
Ƴan Bindiga Sun Sace Tsohon Kakakin Sojin Najeriya
An sace tsohon babban jami’in sojan Najeriya kuma tsohon Daraktan Yada Labaran Tsaro, Rabe Abubakar, tare da matarsa a jihar Katsina. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne ranar Asabar yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani bikin aure, inda ‘yan bindiga suka tare motarsu a yankin Matazu.
Mai magana da yawun sojojin Najeriya, Michael Onoja, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro na ci gaba da kokarin ceto ma’auratan tare da bin diddigin wadanda suka sace su.
Wata majiya ta ce direban motar ya samu nasarar tserewa duk da raunin harbin bindiga da ya samu, yayin da aka tafi da ma’auratan zuwa wani daji da ke kusa da yankin. Lamarin ya zo ne bayan wani hari da aka kai kauyen Kiliya da ke karamar hukumar Dutsinma, inda aka kashe akalla mutane 16 a ranar Juma’a yayin bukukuwan Sallar Layya.
