Featured
NDC Ta Zargi Kwankwaso Da Nuna Wariya Ga Mambobin da Ba Sa Cikin Tafiyar Kwankwasiyya
Wasu shugabannin jam’iyyar NDC na shiyyar Arewa maso Yamma sun zargi tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da yunƙurin mamaye tsarin jam’iyyar a jihar tare da ware mambobin da ba sa cikin tafiyar Kwankwasiyya. Sun ce sun kai ƙorafin ga jagoran jam’iyyar, Seriake Dickson, domin ya shiga tsakani.
A cewar shugabannin, sabani ya fara ne lokacin gudanar da zaɓen shugabannin jam’iyyar a jihar, inda suka yi zargin cewa Kwankwaso ya nemi cikakken iko kan tsarin jam’iyyar. Sun kuma yi ikirarin cewa an hana wasu mambobi damar samun fom ɗin takara, duk da yarjejeniyar da aka ce an cimma kan rabon iko a cikin jam’iyyar.
Sai dai kakakin Kwankwasiyya, Habibu Muhammad, ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa babu wanda aka hana sayen fom ɗin takara saboda jam’iyya ce ke sayar da su ba ƙungiyar Kwankwasiyya ba. Kakaki24 ta ruwaito cewa ya bayyana korafe-korafen a matsayin marasa tushe, yana mai jaddada cewa an bai wa kowa damar shiga tsarin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
