Connect with us

Featured

Ƴan Adawa Ne Ke Zuzuta Matsalar Tsaro Domin Ɓata Sunan Tinubu

Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Muhammad Matawalle, ya zargi ƴan adawar Najeriya da amfani da matsalar tsaro wajen yaɗa farfaganda domin ɓata sunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ya ce manufarsu ita ce cimma muradun siyasa tare da kauda hankalin jama’a daga ci gaban da gwamnati ke samu.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ahmad Dan-Wudil, ya fitar, Matawalle ya ce ana samun gagarumar nasara a yaƙi da rashin tsaro, musamman a yankin Arewa maso Yamma. Ya jaddada cewa babu wata farfaganda ko suka da za su hana shugaban ƙasa ci gaba da cika alƙawuran da ya ɗauka wa ƴan Najeriya.

Ministan ya kuma bayyana cewa Tinubu na da farin jini a Arewacin Najeriya kuma zai samu nasara a zaɓen 2027 saboda irin sakamakon da gwamnati ke samu a yaƙi da ƴan bindiga a jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina, Kaduna da Kebbi. Ya ce al’ummar yankin na ganin sauye-sauyen da ake samu kuma suna goyon bayan matakan da gwamnati ke ɗauka. Kakaki24.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet