Featured
Ma’aikatan Lafiya ‘Yan Najeriya Sama da 10,000 Ne Ke Aiki a Hukumar Lafiya Ta Birtaniya
Wani Sabon Rahoto da aka fitar ya nuna cewa akalla ma’aikatan lafiya ƴan Najeriya 10,494 ne ke aiki a Hukumar Kiwon Lafiya ta Birtaniya (NHS). Adadin ya sanya Najeriya cikin ƙasashen da suka fi samar da ƙwararrun ma’aikatan lafiya ga tsarin lafiyar Birtaniya.
Rahoton ya bayyana cewa yawaitar ƙaura da likitoci, ma’aikatan jinya, masu harhaɗa magunguna da sauran ƙwararrun ma’aikatan lafiya ke yi zuwa ƙasashen waje na ci gaba da ƙara matsin lamba kan tsarin kiwon lafiyar Najeriya, yayin da suke neman ingantaccen albashi da kyakkyawan yanayin aiki.
Read Also : Waiya Ya Tsallaka Zuwa Matakin Ƙarshe a Gasar Masu Magana Da Yawun Jama’a Ta 2026
Masu ruwa da tsaki sun ce wannan ci gaba ya sake tayar da muhawara kan buƙatar yin garambawul domin riƙe ƙwararrun ma’aikatan lafiya a ƙasar da kuma ƙarfafa fannin kiwon lafiya. Kakaki24 ta ruwaito cewa ƙwararrun ma’aikatan lafiyar Najeriya na ci gaba da taka muhimmiyar rawa a tsarin kiwon lafiyar Birtaniya.
