Featured
Kotu Ta Soke Hukuncin Da Ya Ba Wa INEC Umarnin Yi Wa NDC Rajista
Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi ta soke hukuncin da ta yanke a baya wanda ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi wa jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) rijista. A hukuncin da aka yanke ranar 26 ga Yunin 2026, Mai Shari’a Isah Dashen ya ce dole ne a saurari dukkan ɓangarorin da abin ya shafa kafin yanke hukunci.
Kotun ta amince da buƙatar jam’iyyar Peace Movement Party (PMP), tana mai cewa ba a saurare ta ba a shari’ar farko duk da cewa tana da ruwa da tsaki. Hakan ya sa kotun ta bayyana hukuncin da aka yanke a ranar 10 ga Disamban 2025 a matsayin mara inganci, tare da umartar a dawo da shari’ar daga farko.
Read Also : Ma’aikatan Lafiya ‘Yan Najeriya Sama da 10,000 Ne Ke Aiki a Hukumar Lafiya Ta Birtaniya
Kotun ta kuma umarci a ci gaba da sauraron shari’ar tare da haɗa INEC, PMP da NDC a matsayin ɓangarorin da abin ya shafa. Kakaki24 ta ruwaito cewa hakan na nufin duk matakan da aka ɗauka bisa tsohon hukuncin, ciki har da amincewa da rijistar NDC, za su dakata har sai an kammala sabuwar shari’ar.
