Connect with us

Featured

Waiya Ya Tsallaka Zuwa Matakin Ƙarshe a Gasar Masu Magana Da Yawun Jama’a Ta 2026

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya shiga jerin ƴan takara uku na ƙarshe a rukunin ƙwararrun masu bunƙasa harkokin yaɗa labarai a lokutan rikici, a Gasar Masu Magana da Yawun Jama’a ta shekarar 2026. Hakan na ƙunshe cikin sanarwar da shugaban kwamitin shirya gasar, Segun McMedal, ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce Waiya ya kai wannan mataki ne sakamakon gudunmawar da yake bayarwa wajen inganta harkokin yaɗa labarai da sadarwa a Jihar Kano. Ta kuma bayyana cewa mutum 42 ne suka tsallake zuwa matakin ƙarshe a rukuni 16 bayan tantancewa, inda za a fafata domin lashe lambar girmamawar NS Awards.

Read Also : Kwankwaso Ya Ziyarci Obasanjo a Masaukinsa Da Ke Kano

Za a gudanar da bikin bayar da kyaututtukan ne a watan Agustan 2026 a Abuja, ƙarƙashin haɗin gwiwar Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Najeriya (NIPR) da Spokespersons Digest. Kakaki24 ta ruwaito cewa Kwamared Waiya ya taɓa samun lambobin yabo daga ƙungiyoyi da cibiyoyin ƙwararru da dama, ciki har da NUJ, NSB, NIPR da ARCON.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetmatbetimajbetpusulabetvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet