Featured
Kotu Ta Bayar da Belin Shugaban Miyetti Allah Kan Naira Biliyan 2
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta Ƙasa, Bello Bodejo, kan Naira Biliyan 2. Kotun ta kuma umarci ya gabatar da masu tsaya masa biyu da kowannensu zai ɗauki nauyin kuɗin belin iri ɗaya.
Mai shari’a Inyang Ekwo ya ce ɗaya daga cikin masu tsayawa Badejo, dole ne ya mallaki kadara a yankin Abuja Municipal Area Council (AMAC), sannan ɗaya daga cikinsu ya gabatar da shaidar biyan haraji na shekarun 2023, 2024 da 2025. Haka kuma kotun ta umarci magatakarda ya tantance dukkan takardun kafin a cika sharuddan belin.
Read Also : Shettima Ya Tafi Saliyo Domin Wakiltar Tinubu a Taron ECOWAS
Kotun ta kuma umarci Bello Bodejo ya miƙa fasfo ɗinsa tare da hana shi fita daga Najeriya ko wajen ikon kotun ba tare da izini ba. Daga nan kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranakun 5, 6 da 7 ga Oktoban 2026, yayin da yake fuskantar tuhume-tuhume 12 da suka shafi zargin zambar kuɗaɗe da suka kai dala miliyan 2.33.
