Featured
Kwale-kwale Ya Kife Da Mata Da Yara Kimanin 40 a Jigawa
An tabbatar da mutuwar mutum guda bayan wani kwale-kwale da ke ɗauke da mata da yara kimanin 40 ya kife a yankin Malamawa ta ’Yan Dutse, Ƙaramar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa. Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 19 Yuli, 2026.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, SP Shi’isu Lawan Adam, ya ce rahotannin farko sun nuna cewa kwale-kwalen na ɗauke da mata da yara kusan 40 lokacin da ya kife. Ya ce an gano gawa guda, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da neman sauran fasinjojin da ba a gano inda suke ba.
Read Also : Kotu Ta Bayar da Belin Shugaban Miyetti Allah Kan Naira Biliyan 2
Masarautar Ringim ta kuma tabbatar da aukuwar hatsarin, tana mai cewa ana ci gaba da tattara sahihan bayanai domin tantance adadin waɗanda suka mutu da kuma waɗanda aka ceto. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomi ba su fitar da cikakken adadin waɗanda suka tsira ko suka rasa rayukansu ba, yayin da ake ci gaba da bincike kan musabbabin hatsarin.
