Featured
Mun kusa kawo ƙarshen zazzaɓin cizon sauro a Najeriya – Gwamnatin Tarayya
Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a na Nijeriya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu ta ƙuduri aniyar kawo ƙarshen zazzabin cizon sauro a ƙasar, tare da ƙara zuba kuɗaɗe a fannin kiwon lafiya.
Pate ya ce ƙara saka hannun jari a fannin kiwon lafiyar na da muhimmanci domin rage dogaro da tallafin ƙasashen waje wajen yaƙi da cututtuka.
Gidan Talabijin na NTA ya ruwaito cewa ministan ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake karɓar tawagar Kwamitin Amintattu na Malaria Consortium, wadda ta kai ziyara Ma’aikatar Lafiya.
Pate ya bayyana cewa an samu raguwar yawan yara masu ɗauke da kwayar cutar zazzabin cizon sauro daga kashi 42 cikin 100 a shekarar 2010 zuwa kashi 15 cikin 100 a shekarar 2025.
