Featured
Zaɓen 2027 : Ɗan takarar gwamnan Kano a ADC ya zaɓi ɗan shekara 36 a matsayin mataimakinsa
Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Alhaji Ibrahim Alamin Little, ya bayyana Abdulkadir Shehu Bari mai shekaru 36, daga Ƙaramar Hukumar Rogo a matsayin abokin takararsa na mataimakin gwamna a zaɓen 2027.
Little ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a Kano yayin wani taron manema labarai, inda ya ce ya zaɓo matashi ne domin ba wa matasa dama wajen ganin an dama da su a sha’anin mulkinsa, ya kuma yi alƙawarin ba da fifiko ga ilimi, kiwon lafiya, ƙarfafa matasa da mata idan aka zaɓe shi a matsayin gwamnan jihar.
Ya ce gwamnatinsa za ta magance matsalolin da suka addabi ɓangarorin ilimi da lafiya, tare da yaƙi da matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi tsakanin matasa. Ya kuma yi alƙawarin samar da shirye-shiryen jinƙai ga zawarawa, marayu da yaran da ba sa zuwa makaranta.
A nasa ɓangaren, ɗan takarar mataimakin gwamnan ya ce zai kokari ya ga cewa bai ba wa matasa kunya ba, kazalika za su yi duk mai yiwuwa idan suka yi nasara a 2027, wajen ganin matasa sun samu kyakkyawar rayuwa a jihar Kano da ma Najeriya baki daya.
