Connect with us

Featured

Kwanaki 87 da sace ɗalibai a Borno, shin ina aka kwana ?

Kwanaki 87 kenan tun bayan da ’yan ta’adda suka sace ɗalibai a Mussa Primary da Junior Secondary School da ke Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno, iyalan yaran na cigaba da kasancewa cikin ƙunci da raɗaɗin rashin ƴaƴan nasu.

Iyayen yaran sun bayyana cewa tun bayan sace su a ranar 15 ga Mayu 2026, ba su samu wani sahihin bayani daga hukumomi kan inda ’ya’yansu suke ko halin da suke ciki ba. A cewarsu wannan rashin bayanai na ƙara jefa su cikin damuwa da fargaba.

Read Also : Sau ɗaya Tinubu yake cin abinci a kullum, wani lokacin ma da ƙafa yake zuwa ofis – Shugaban NRS

Shugaban iyayen yaran, Ishaya Suya, ya ce rayuwa ba tare da ’ya’yansu ba azaba ce, yana mai cewa ba su san ko yaran suna lafiya, suna samun abinci ko kuma suna fama da rashin lafiya ba. Ƙungiyar ƙungiyoyin fararen hula ta Borno ma ta yi Allah-wadai da shiru da hukumomi suka yi, tare da neman a gaggauta ceto yaran.

Wani jami’in tsaro da ke cikin aikin ceto ya bayyana cewa an fuskanci kwanton ɓauna a  yunƙurin farko da jami’an tsaro, mafarauta da ’yan banga suka yi, inda aka gano wayoyin salula sama da 30 a wani masallaci da ke cikin daji. Gwamnatin Borno ta ce batun na tsaro ne, yayin da wani ƙwararren tsaro ya bukaci gwamnatin tarayya ta ƙara himma wajen ganin an kuɓutar da yaran.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet