Featured
Wike Ya Musanta Neman Shugabancin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu a 2027
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya musanta rahotannin da ke cewa yana neman zama Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaba Bola Tinubu na jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Wike ya sake jaddada goyon bayansa ga sake zaɓen Shugaba Tinubu, yana mai cewa ba ya buƙatar wani matsayi a kwamitin yaƙin neman zaɓen domin taimaka wa shugaban ƙasa samun nasara a Jihar Rivers da Abuja.
Read Also : Kwanaki 87 da sace ɗalibai a Borno, shin ina aka kwana ?
A cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Sadarwar Jama’a da Kafofin Sada Zumunta, Lere Olayinka, ya fitar ranar Litinin, Wike ya ce rahoton ƙarya ne. Ya kuma bayyana cewa bai tattauna da kowa kan shugabanci ko kasancewa mamba a kwamitin yaƙin neman zaɓen ba.
Wike ya ce a halin yanzu ba ya cikin Najeriya, domin ya fita waje hutawa, bayan shafe sama da kwanaki 30 yana ƙaddamar da ayyuka da duba wasu ayyukan raya ƙasa. Ya ce bayan dawowarsa, zai mayar da hankali wajen ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnatin Tinubu da kuma tabbatar da nasarar shugaban a Rivers da Abuja.
