Connect with us

Featured

AFAN ta yaba wa shugaba Tinubu kan inganta harkar noma da taimakawa manoma a Najeriya

Ƙungiyar Manoman Najeriya (AFAN) ta yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka wajen inganta tsaro da sauya fasalin harkar noma a ƙasar. Shugaban AFAN na ƙasa, Farouk Rabiu Mudi, ya ce haɗin gwiwar ƙungiyar da gwamnati na taimakawa wajen dawo da manoma gonakinsu da bunƙasa samar da abinci.

Mudi ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da aka gudanar ranar Talata 18 ga Agusta, ya ce Najeriya na da sama da hekta miliyan 70 na filayen noma, sai dai matsalolin tsaro sun hana amfani da wasu daga cikinsu yadda ya kamata. Ya ce haɗin gwiwar AFAN da Ma’aikatar Tsaro ta ƙasa ya taimaka wajen komawar manoma gonakinsu, tare da sauƙaƙa halin da wasu mutanen da ke sansanonin ‘yan gudun hijira ke ciki.

Read Also : Kano Govt Faults TRACKA Report on ₦235.4m School Project

Ya kuma bayyana cewa AFAN na shirin shirya Baje Kolin Noma na Ƙasa da Ƙasa tsakanin Najeriya da Brazil a Kano a watan Nuwamba, tare da haɗin gwiwar gwamnatin Kano da KACCIMA. A cewarsa, taron zai samar da damar musayar ilimi, fasaha da sabbin dabaru, tare da taimakawa wajen sauya noma daga tsarin gargajiya zuwa noma na zamani mai amfani da injuna.

Shugaban AFAN ya kuma yabawa Tinubu kan kafa Ma’aikatar Noma da Samar da Wadatar Abinci da wasu tsare-tsaren tallafa wa noma, ciki har da NAGS-AP, asusun bunƙasa noma da Bankin Noma. Ya ce idan aka ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu da abokan hulɗar ci gaba, Najeriya za ta iya zama babbar cibiyar noma a Afirka ta Yamma.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet