Featured
NDLEA Ta Kama Mutane 80, Ta Tarwatsa Wuraren Cinikayyar Miyagun Ƙwayoyi 16 a Kano
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta ce ta kama mutane 80 tare da tarwatsa wuraren cinikayyar miyagun ƙwayoyi 16 cikin kwanaki bakwai na Operation Restore Order.
Jami’in Yaɗa Labaran hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari, ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Talata 18 ga Agusta 2026. Ya ce an ƙaddamar da aikin ne ranar 10 ga Agusta.
Read Also AFAN ta yaba wa shugaba Tinubu kan inganta harkar noma da taimakawa manoma a Najeriya
Sanarwar ta ce samamen ya gudana daga 10 zuwa 16 ga Agusta a wurare daban-daban da ake zargin sun zama wuraren cinikayya da shan miyagun ƙwayoyi, ciki har da Filin Mahaha, Koki, Dorayi, Rijiyar Lemo, Kasuwar Kurmi, Zage, Gwammaja da Farm Center.
NDLEA ta ce jami’anta sun kwato Cannabis sativa, Diazepam, Exol 5, rubber solution da wasu miyagun ƙwayoyi. Waɗanda aka kama za su fuskanci bincike da gurfanarwa, yayin da hukumar za ta ci gaba da sanya ido kan wuraren da aka tarwatsa.
