Connect with us

Featured

NDLEA Ta Cafke Wani Fitaccen Ɗan Kasuwa Kan Zargin Safarar Hodar Iblis Ta Naira Biliyan 39

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta cafke fitaccen ɗan kasuwa Afolabi Kazeem Michael, wanda aka fi sani da KC Luxury, bisa zargin hannu a safarar hodar iblis daga Kudancin Amurka zuwa Najeriya da wasu ƙasashen duniya.

An cafke KC Luxury ne a ranar 13 ga Agusta a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, yayin da yake shirin tafiya Paris. Wannan ya biyo bayan binciken da hukumar ta gudanar kan wani kaya da aka cafke ɗauke da kilo 184.5 na hodar iblis, wadda aka kiyasta darajarta da kusan Naira biliyan 39.

Read Also : Jihohi 31 Sun Kashe Naira Biliyan 252 Wajen Ƴaƙi da Rashin Tsaro a Cikin Watanni Shida – Rahoto

NDLEA ta ce an ɓoye hodar iblis ɗin ne a cikin wani kaya da ake shirin fitarwa daga Najeriya ta hannun wani kamfanin jigilar kaya. Hukumar ta ce binciken da ya biyo bayan kamen ya kai ga cafke wasu mutane da ake zargi da hannu, yayin da jami’ai suka samu KC Luxury da Yuro 7,750, Fam 2,800 da Naira 100,000 tare da wasu kayan ado masu tsada.

Hukumar ta ƙara da cewa binciken da aka gudanar a gidansa da ke Banana Island ya kai ga ƙwace wasu motocin alfarma. NDLEA ta ce binciken ya gano hanyar safarar hodar iblis tsakanin Kudancin Amurka, Najeriya, Birtaniya da wasu ƙasashen Turai da Asiya, inda aka kama wasu da ake zargi da hannu a Birtaniya.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet