Connect with us

Featured

’Yan Bindiga Sun Sace Shugaban APC a Karamar Hukumar Rogo

Wasu ’yan bindiga sun kai hari a yankin ƙauyen Beli da ke kusa da garin Zarewa a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano, inda suka kashe wani almajiri tare da sace shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar, Alhaji Abdullahi Beli.

Rahotanni sun ce maharan sun kutsa ƙauyen Beli ne a daren Litinin, inda suka sace Abdullahi Beli daga gidansa jim kaɗan bayan ya dawo daga wani taron jam’iyya a Zarewa. Harin ya kuma haddasa harbe-harbe da firgici a cikin ƙauyen.

Read Also : EFCC ta kori ma’aikata sama da 40 sakamakon zargin cin hanci

Sakataren yaɗa labarai na APC a jihar Kano, Auwalu Sojo, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa Abdullahi na hannun masu garkuwa da shi, yayin da jami’an tsaro suka fara aikin ceto bayan sanar da su aukuwar lamarin.

A baya bayan nan dai wasu hare-haren ’yan bindiga a Kano sun yi sanadin mutuwar mutane da dama, ciki har da shugaban APC na mazabar Rantan a karamar hukumar Bebeji, Alhaji Garba Buba, yayin da wasu maharan suka kashe mutum uku tare da jikkata biyar a ƙauyen Chiromawa na karamar hukumar Garun Malam.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet