Connect with us

Featured

NDC za ta nemi gudummawar kuɗi daga ƴan Najeriya domin gudanar da yaƙin neman zaɓe

Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta ce za ta tara kuɗin gudanar da yaƙin neman zaɓenta na 2027 ne ta hanyar gudummawar talakawan Najeriya, maimakon dogaro da attajirai da masu ɗaukar nauyin ’yan siyasa.

Jagoran jam’iyyar na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, ya ce za a bai wa ’yan Najeriya damar bayar da gudummawar kuɗi daga N1,000 zuwa N2,000 domin tallafa wa yaƙin neman zaɓen jam’iyyar. Ya ce hakan zai rage tasirin masu hannu da shuni kan harkokin siyasar ƙasar.

Read Also : Trump ya yi alƙawarin ba wa kowane ɗan Amurka $5,000 idan jam’iyyar Republican ta yi nasara

Dickson ya bayyana haka ne yayin wata hira da Arise News, inda ya ce jam’iyyar na son samar da tsarin da zai bai wa kowa damar taka rawa a harkar siyasa, ba tare da la’akari da halin kuɗinsa ba. Ya kuma ce NDC ba ta samun kuɗin gudanar da ayyukanta daga baitulmalin gwamnati.

Ya ce jam’iyyar za ta kai manufofinta kai tsaye ga ’yan Najeriya, kuma ba za ta ɗauki wata ƙuri’a da wasa ba. Dickson ya kuma bayyana cewa ana tuntubar juna kan waɗanda za su shiga kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na NDC, yayin da ya buƙaci INEC da hukumomin tsaro su tabbatar da an gudanar da zaɓen 2027 cikin ’yanci da adalci.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet