Connect with us

Featured

Rundunar ƴansandan Kano ta kama mutane biyu da ake zargi da hannu a mutuwar Ibrahim Ɗanshagamu

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane biyu, da ake zargi da hannu a mutuwar Ibrahim Khalil Danshagamu, mazaunin unguwar Gaida da ke Karamar Hukumar Kumbotso.

Rundunar ta ce a ranar Litinin, 8 ga Satumban da muke ciki, da misalin ƙarfe 11:30 na dare, ta samu rahoton cewa, wasu ’yan daba sun kutsa gidan marigayin, inda suka yi masa munanan raunuka. An garzaya da shi Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Read Also : Rundunar Ƴansanda ta kama matar da ta ƴada takardar cewa Kamfanin OPay zai dakatar da ayyukansa

Bayan umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, DPO na Kumbotso tare da rundunonin dabaru da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma, sun gudanar da samame bisa bayanan sirrin da aka samu, wanda ya kai ga cafke waɗanda ake zargin. A halin yanzu suna hannun ’yan sanda, kuma da zarar an kammala bincike za a gurafanar da su a gaban kotu.

Kwamishinan ya jajanta wa iyalan marigayin, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙarin gano duk waɗanda ke da hannu a lamarin domin gurfanar da su a gaban kotu. Rundunar ta kuma ƙara sintiri da tattara bayanan sirri a Gaida da kewaye, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da kai rahotannin da za su taimaka wajen tabbatar da tsaro.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet